Wednesday, 7 November 2018

'Yan shekara 29 sun lashe zaben majalisar dokoki

Alexandria Ocasio-Cortez da Abby Finkenauer - dukkansu 'yan shekara 29 - na kan hanyarsu ta zama mata mafi karancin shekaru da aka zaba a matsayin 'yan majalisun dokokin Amurka.


Ocasio-Cortez, wacce ake yi wa lakabi da tauraruwa mai haskawa a Jam'iyyar Democrat ta lashe zabe ne da kuri'u fiye da kashi 78 a gunduma a 13 da ke birnin New York.

Ms Finkenauer ta samu da kashe 50 cikin dari na kuri'un da aka kada a gunduma ta farko ta jihar Iowainda ta kayar da dan jam'iyyar Republican Rod Blum.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment