Sunday, 18 November 2018

'Yan takarar gwarzon dan kwallon kafar Afirka na BBC na 2018

An bayyana sunayen 'yan wasa biyar da a cikinsu za a zabi gwarzon dan kwallon kafar Afirka na BBC na bana.


'Yan takarar gasar a wannan shekarar su ne: Medhi Benatia (dan kasar Moroko) da Kalidou Koulibaly (dan kasar Senegal) da Sadio Mane (shi ma daga Senegal) da Thomas Partey (dan kasar Ghana) da kuma Mohammed Salah (wanda dan kasar Masar ne).

Za a fara kada kuri'a a ranar Asabar, 17 ga Nuwamba da karfe bakwai na yamma agogon GMT.

Kuma a rufe gasar a ranar 2 ga watan Disamba karfe takwas na yamma agogon GMT.

Za a bayyana sakamakon gasar ne a wani shirin tashar BBC,mai yada shirye-shiryenta zuwa kasashen duniya, a ranar 14 ga watan Disamba da karfe biyar da rabi agogon BST.

Wani kwamitin kwararru kan harkokin kwallon kafa na Afirka ne suka fitar sunayen 'yan wasan biyar.

Dan wasan gaban Liverpool, Salah, shi ne ya lashe gasar a bara.

'Yan wasa kamarsu: Jay-Jay Okocha da Michael Essien da Didier Drogba da Yaya Toure da kuma Riyad Mahrez su ma sun taba lashe gasar a baya.

'Yan wasa biyar din da ke takarar
Dan wasa mai tsaron baya na Juventus, Benatia, mai shekara 31, ya lashe gasar Lig sau hudu a jere a bana - biyu tare da Bayern Munich da kuma sauran biyun tare da Juve.
Kuma ya jagoranci Moroko a gasar cin kofin duniya ta bana.

Dan wasan baya na Napoli, Koulibaly, mai shekaru 27, ya yi iya kokarin ya ga kulob dinsa ya samu nasara tare da Juve domin cin gasar Serie A.

Ya buga dukkannin wasannin da Senegal ta yi a gasar cin kofin duniya.
Dan wasan gaban Liverpool, Mane, mai shekara 26, shi ma ya buga dukkannin wasannin da Senegal ta yi a gasar cin kofin duniya na bana.

Ya jagoranci kasarsa wajen cin kwallaye biyu a wasansu da Japan.
Dan kwallon shi ne na biyu da ya fi cin kwallaye a gasar zakarun Turai a kakar bana - ya ci wa Liverpool 10 ciki har da wasan karshe da Real Madrid ta doke su da ci 3-1.

Dan wasan tsakiyar Atletico Madrid Partey, mai shekara 25, yana cikin 'yan wasa 11 da kocin kungiyar Diego Simeone yake fara wasa da su.

Dan kwallon ya taka leda wasan karshe na gasar Europa, inda Atletico Madrid ta doke Marseille.

Kuma ya ci wa Ghana kwallo a karawarsu da Japan da kuma Icelend.
Dan kwallon gaba na Liverpool, Salah, mai shekara 26, ya zama dan wasan da ya fi kowanne cin kwallaye a gasar firimiya, inda ya ci kwallaye 32 a watan Mayu.

Kuma kamar Mane, ya ci kwallaye 10 a gasar cin kofin zakarun Turai, kungiyar Real Madrid ce ta doke su a wasan karshe.

Salah ne ya zura duka kwallayen da Masar ta ci a gasar cin kofin duniya.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment