Tuesday, 27 November 2018

'Yan wasana basu bin umarnina>>Mourinho

Me horas da 'yan wasan kunguyar Manchester United, Jose Mourinho ya bayyana cewa yana takaicin irin yanda 'yan wasanshi ke bijirewa umarnin da ya basu idan suka shiga fili suna taka leda.


Mourinho ya bayyana hakane a wata tattaunawa da aka yi dashi kamar yanda ESPN ta ruwaito, a yaune dai Man U zata kara da Young Boys a filinta na Old Trafford a ci gaba da gasar cin kofin zakarun turai sannan a cikin wasanni 9 da Man U ta buga a gida guda uku ne kawai ta yi nasara.

Mourinho ya bayyana cewa, nakan so 'yan wasana su fara wasa kan jiki kan karfi da abokan hamayya, su kai musu hari da farko ba wai su tsaya suna jira ba.

Ya kara da cewa, ku 'yan jarida da 'yan kallo kuna tunanin wai ni ke gayawa 'yan wasana su fara wasa a hankali ko kuma su tsaya jira sai an fara kawo musu hari tukuna amma ba haka bane basa yin abinda nike gayamusu ne kuma abin akwai ban takaici.

Ya kara da cewa, yana son buga wasan yau tun da mintinan fari kamar wasa na gaske wanda idan basu yi nasara ba akwai matsala, yace yana son 'yan wasan su buga wasan kamar suna yi kada su dauki abokan karawar nasu sakwa-sakwa.

Haka kuma Mourinho ya bayyana cewa hankalinshi be tashi idan yana buga wasa a gida kamar yanda wasu ke tunani, yace rashin girmamawane ga filin Old Trafford da 'yan kallo wai ace shi ko kuma 'yan wasan hankalin su na tashi idan zasu buga wasa a gida.

Ya kara da cewa duk dan wasan da yasan hankalinshi na tashi idan zai buga wasa a gida to yau kada ya fito ya zauna a gidanshi ya kalli wasan nasu a talabijin.

No comments:

Post a Comment