Friday, 16 November 2018

Yanda akawa Sanata Shehu Sani fashin tikitin takarar sanatan Kaduna ta tsakiya

Rahotanni sun bayyana yanda aka kwace tikitin tsayawa takarar sanatan Kaduna ta tsakiya na jam'iyyar APC daga hannun Sanata Shehu Sani aka baiwa na hannun damar gwamnan jihar, Uba Sani.

Shafin Sahara Reporters ya ruwaito cewa dala miliyan 2 aka sayi tikitin na Sanata Shehu Sani kuma wata tahannun damar gwamnan, shugabar hukumar kula da gabar ruwa ta kasa, Hadiza Bala Usman ce takai gwauro takai mari, ta bayar da kudin akan kwace tikitin daga hannun Sanata Shehu Sani.

Sahara Reporters ta kara da cewa har kwana sai da gwamna El-Rufai yayi a ofiahin shugaban jam'iyyar ya kuma yi barazanar ficewa daga APC idan ba'a kwace tikitin daga hannun Sanata Shehu Sani ba.

A karshe dai gwamnan ya samu abinda yake so

No comments:

Post a Comment