Wednesday, 7 November 2018

'Yansandan farin kaya sun kama shugaban APC, Adams Oshiomhole

Wani labarai da ya dauki hankulan 'yan Najeriya shine me cewa hukumar 'yansandan farin kaya ta DSS ta kama shugaban jam'iyya me mulki ta APC, Adams Oshiomhole bisa zargin aikata ba daidaiba a zaben fidda gwanin jam'iyyar.


Lamarin ya farune ranar Lahadin da ta gabata, kamar yanda jaridar The Cable ta ruwaito inda tace 'yan sandan na farin kaya sun tsare Oshiomhole har na tsawon awanni 9 inda suka mai tambayoyi akan zargin da wasu gwamnonin APC ke mishi na karbar cin hanci lokacin zaben fidda gwani da aka yi na jam'iyyar a fadin kasarnan.

A karshe sun bukaci Oshiomholen da ya yi murabus daga mukamin nashi, saidai ya ki ya yace musu bazai yi murabus ba saidai idan Shugaba Buharine ya bukaci hakan.

Ranar Litinin, Oshiomhole ya garzaya fadar shugaban kasa inda ya zayyana mishi abinda ya faru, rahoton yace Buhari yayi matukar mamaki da jin wannan lamarin inda yace besan hakan ta faru ba amma zai bincika.

No comments:

Post a Comment