Thursday, 29 November 2018

Yau za'a fara shagalin bikin Priyanka Chopra da Nick Jones, idan kaji yawan kudin da za'a kashe sai ka rike baki

A ranar 29 ga watan Nuwambar 2018 ne za a fara gagarumin bikin da jama'a da dama a fadin duniya suka jima suna jiran zuwansa.


Wannan bikin dai shi ne bikin jarumar fina-finan kasar Indiya Priyanka Chopra da Nick Jones, wanda mawaki ne dan kasar Amurka.

Bikin zai fara kankama ne daga ranar biyu da uku ga watan Disamba.

Masoyan junan za su yi biki nau'i biyu, wato da na al'adar Hindu, wanda shi za a fara, sai kuma biki irin na kiristanci da za a yi washegari.

Za a shafe kwana biyar ana wannan kasaitaccen biki wanda za a yi shi a wani katafaren otel na Taj Umaid Bhawan da ke Jodhpur a kasar India.

Wannan otel dai na alfarma ne, domin sai wane da wane ke zuwa wajen, amma kuma rahotanni sun ce ma'auratan sun karbe kusan dukkan dakunan otel din saboda bakinsu masu zuwa wajen bikin.

Dangane da lissafin da aka yi na kudaden dakunan da aka kama a otel din, da abincin da za a ci da amfani da dakunan taron otel din da dai sauransu, an kiyasta cewa za a kashe kusan crore hudu a tsawon kwana biyar, kwatankwacin dala miliyan 60.

Dangantaka tsakaninta da Nick Jones
A watan Mayun da ya gabata ne masoyan junan suka bayyana wa duniya cewa suna soyayya.

Amma kuma tun a 2017, suka san juna har suke dan gaisawa.

Akwai dai tazarar shekaru a tsakanin Priyanka da Nick Jones, inda ita ta bashi ratar shekara tara, ita yanzu haka tana da shekara 36, shi kuma 27.

To amma hausawa kan ce so baya hana ganin shekaru.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment