Friday, 2 November 2018

Za A Kafa Rundunar JTF A Zamfara

Duk da rundunonin soji tare da jiragen yaki da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta tura a jihar Zamfara, ana ci gaba da samun yawaitar ayyuka ‘yan bindiga, kama daga kai hare-hare, da kisan jama’a, har ma da satar mutane domin karbar kudin fansa, wanda a yanzu ya zama ruwan dare a jihar.


To sai dai gwamnan jihar Abdul aziz Yari Abubakar, ya ta’allaka wannan yanayin da rashin iya game dukkan yankunan jihar a lokaci daya da jami’an tsaron, duk kuwa da yawan da suke da shi.

A kan haka ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki akan sha’anin tsaro a Gusau babban birnin jihar, Gwamna Yari ya bada sanarwar matsayar da aka cimma ta kafa rundunar hadin gwiwa da farar hula, wato “Civilian JTF” a turance, a karkashin jagorancin hukumomin tsaro a jihar.

Tuni da aka yi haramar samar da dokar kafa sabon tsarin a majalisar dokokin jihar, inda za’a dauki matasa kusan 8,500 da za’a horar da su, tare kuma da biyansu alawus na naira 15,000 a kowane wata, kari ga alkawarin bada tukuicin naira miliyan daya ga duk wanda ya kama dan ta’adda mai bindigar AK47.
VOAhausa.

No comments:

Post a Comment