Thursday, 15 November 2018

Za Mu Biya Sabon Albashi Amma Za Mu Rage Ma'aikata>>Kungiyar Gwamnoni

Kungiyar gwamnonin Nijeriya ta jaddada cewa za ta iya biyan albashi mafi karanci na 30,000 ne kawai idan har kungiyar Kwadago ta amince gwamnonin su rage yawan Ma'aikata.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin kuma Gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari ya ce, kwamitin karin albashin bai tuntubi gwamnoni ba kafin ya cimma matsaya kan sabon albashin inda ya nuna cewa dole sai gwamnatin tarayya ta karawa jihohin kasafinsu na asusun tarayya idan har tana son su biya sabon albashin.
Rariya.

No comments:

Post a Comment