Wednesday, 28 November 2018

Za'a fara samar da wutar lantarki da kashin Aladu

Wasu masana kimiyya a kasar Amurka na shirin fara samar da wutar lantarki daga kashin aladu, masanan da suka fito daga jihohin Carolina da Virginia sun ware kudi dala miliyan 250 dan ganin wannan shiri nasu yayi nasara.


Bloomberg ta ruwaito cewa masanan zasu hada hannu ne da manoma aladun ta yanda zasu rika samun kashin cikin sauki suna sarrafashi ya koma gas daga nan kuma sai a rarabashi zuwa gidaje da guraren kasuwanci ta hanyar bututu dan amfanin al'umma.


No comments:

Post a Comment