Thursday, 15 November 2018

'Zargin Da Buhari Ya Yi Kan Kwankwaso Ba Gaskiya Ba Ne'

Dalibin nan da ya yi wa Sanata Kwankwaso wakar turanci ya aika wa Kwankwason da wata wasika sannan kuma ya mayar da martani ga shugaba Muhammadu Buhari akan furucin da ya yi akan Kwankwaso a Paris.


Da farko dai ina aika sako zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya maida hankali wajen yin ayyukan raya kasa da gina talakawan Nijeriya musamman a bangaren yankin mu na arewac. Domin a mulkin Shugaba Muhammadu Buhari mu a bangaren mu na arewa tuni an riga an bar mu a baya wajen samun manyan ayyuka daga gwamnatinsa. 

Domin kada ya kasance mun tura mota kuma da ta tashi sai ta bade mu da hayaki. Ta haka ne kawai shugaban kasa zai iya samun farin jini a wajen al'ummar kasa bayan ya gama mulki kamar yadda Dr Rabiu kwankwaso a kullum yake samun karuwar magoya baya a fadin kasar nan. Gashi dai ya gama Gwamna amma babu wani gwamna a duk Nijeriya mai ci a yanzu da ya kai Rabiu Kwankwaso yawan magoya baya. Saboda haka gaskiya da rikon amana ce ta jawowa Kwankwaso haka.

Abinda shugaban kasa ya fada akan Dr Rabiu Kwankwaso ba gaskiya bane, kowa ya san hassada ce ake masa saboda Allah ya daukaka Kwankwaso kuma ya ba shi farin jinin al'umma. Kuma kowa ya san shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saba kwan gaba kwan baya a maganganunsa. Saboda haka abinda shugaban kasa ya fada siyasa ce kawai amma ba gaskiya bane.

Abu na biyu shine ina maka (Dr Rabiu kwankwaso) barka da zuwa Kano. Kuma da fatan ka koma lafiya. Allah ya kara maka imani da tausayin talakawan Nijeriya. Allah kuma ya dora ka akan dukkanin makiyanka, ya kuma raba ka daga sharrinsu.

Baba Kwankwaso ka sani ina son ka saboda Allah. Babu wani mutum ko dan siyasa da ya saka min kaunar ka a cikin zuciyata. Soyayyar da nake maka ta samo asali ne a sanadin ayyuka na alkairi da ka yi wa jihar Kano da kuma mutanen jihar Kano gaba dayansu, musamman ma 'ya'yan talakawa wadanda ka dauke su tamkar 'ya'yan da ka haifa a cikinka. Mai girma jagora a sanadinka na ga 'ya'yan talakawa da yawa, wasu ma daga cikin su marayu ne amma sun sami damar da yayan masu fada aji ma sai sun yi da gaske sannan za su iya samun wannan damar. 'Ya'yan talakawa wadanda yawansu ba shi da adadi sun yi ilimi, sun yi aure, sun yi kudi, sun gina gidaje, kuma suna taimakawa iyayensu duk a saboda irin kyakykyawan shugabanci na adalci da kayi a jihar Kano.

Mai girma Sanata kuma jagora, ina son ka sani cewa duk abinda zan fada akanka to abu ne wanda ka riga ka yi shi, ya faru, kuma kowa ya san ya farun. Babu kage ko kadan a tsakani na da Kai. Duk abinda na sani akanka to abune na alkairi, abu ne mai kyau. Wallahi ni ban san laifin ka ba. Duk abinda wasu daga cikin makiyanka suke fada na laifin ka wallahi kage ne, domin na bincika na gani bai tabbata Ba. 

Mai girma Sanata da a ce kana da laifin da ya kamata a fito a fada domin ka gyara, to wallahi da zan fito na fada maka gaskiya komai dacin ta. Domin hakan shine cikakken so na gaskiya. Kuma Baba ka kara hakuri, insha Allah shugabancin Nijeriya uwa ka yi shine ka gama. Lokaci kawai muke jira. Akwai tanadin da Allah ya yi maka. Jama'ar Kano da ta Nijeriya duk naka ne Baba.

Mai girma jagora ina maka albishir da cewa dan takarar Gwamna da ka tsayar mana a Kano wato Abba Kabir Yusif mun yi farin ciki da zabinka, kuma mu mutanen Kano mun karbi Abba hannu bibbiyu. Muna masa fatan alkairi. Allah ya sa zabin ka ya zamo mafi alkairi ga jihar Kano da mutanen cikinta gaba daya. Kuma insha Allahu za mu zabi Abba. Da yardar Allah sai mun kifar da APC da PRP da ma kowacce irin jam'iyya a jihar Kano. 

A karshe ina maka fatan alkairi. Allah ya yi maka albarka, ya kara daukaka. Allah ya raba ka daga sharrin makiyanka na fili da na boye. Allah ya kara maka imani da tausayi. Allah ya kara maka soyayyar Annabi Muhammad SAW. Allah yasa aljanna ce makomarka. Amin ya rabb.

Daga Mustapha Abdullahi Inuwa Jauben Gadanya, Kano
08133398649

Ina gaishe da jama'ar jihar Kano dama na Nijeriya

No comments:

Post a Comment