Friday, 30 November 2018

ZARGIN WULAKANTA KUR'ANI A ZAMFARA: Kotu Ta Yankewa Tsohon Shugaban Jam'iyyar APC Na Gusau Hukuncin Kisa

Wata babbar kotun musulunci dake garin Gusau na jihar Zamfara ta yanke hukuncin kisa ga tsohon shugaban jam'iyyar APC na Sabongari Gusau, wato Mainasara Yahaya da wani mutum daya bisa laifin wulakanta Alqurani, inda suka yayyaga shi da jefawa cikin bayan gida.


Wadanda ake zargin sun aikata wannan laifi ne a shekarar 2017. 

Yanzu dai abun jira a gani shine Gwamna Abdul-aziz Yari Abubakar ya saka hannu a aiwatar da wannan hukunci.

Daga Real Sani Twoeffect Yawuri

No comments:

Post a Comment