Wednesday, 26 December 2018

A karin farko Ronaldo zai sha zaman benci a Juventus

Me horas da kungiyar Juventus, Massimiliano Allegri ya bayyana cewa, tauraron dan kwallon kungiyar, Cristiano Ronaldo ba zai buga wasan su da Atlanta ba na yau, Laraba da zasu buga ba.


Wannan ne dai karin farko da Ronaldon zai sha zaman benci tun bayan da ya koma kungiyar ta Juve daga Real Madrid.

Massimiliano Allegri yace Ronaldo zai zauna tare dashi a wajen fili su yi kallon wasan na yau tare, ya bayyana cewa Ronaldon zai hutane dan kara shiryawa wasan gasar cin kofin zakarun turai da zasu buga.

Ga dukkan alamu dai Massimiliano Allegri yana tsoron kada a samu kuskurene Ronaldon ya samu rauni kamin wasansu me muhimmanci da zasu buga da Atletico Madrid a gasar cin kofin zakarun turai.

No comments:

Post a Comment