Thursday, 6 December 2018

A'isha Buhari ta nesanta kanta da wanda ake zargin yaudarar mutane da sunanta

Uwargidan shugaban kasa, Hajiya A'isha Buhari ta bayyana cewa, tana bibiyar binciken da hukumar 'yansandan farin kaya, DSS ke yi akan yaudarar mutane kudi da aka kama wata mata na yi da sunan ofishinta.


A'isha ta bayyana cewa, bata da alaka da mutanen da ake zargin sannan kuma ba'a kasuwanci a ofishinta duk wanda ya yarda aka yaudareshi da haka to shi ya jiyo.

Sannan tace duk ma'aikacin ofishinta da aka kama na da hannu a wannan badakala zai fuskanci fushin hukuma.

No comments:

Post a Comment