Wednesday, 5 December 2018

Akwai wasu mutane biyu dake hana Buhari yin aiki yanda ya kamata>>A'isha Buhari

Uwargidan shugaban kasa, Hajiya, A'isha Buhari ta bayyana cewa, akwai wasu mutane masu karfin fada aji su biyu a gwamnatin mijinta dake hana shi yin aiki yanda ya kamata.


A'isha Buhari ta bayyan hakane jiya, Laraba a gurin wani taro da kungiyar 4+4 ta shirya a babban birnin tarayya, Abuja, kamar yanda shafin persecondnews.com ya ruwaito.

A'isha bata bayyana sunayen mutanen ba amma tace abinda ke kara bata haushi shine irin yanda sauran mutane maimakon su yi maganin mutanen nan guda biyu sai su rika tururuwa gurin su neman Alfarma.

A'isha tace akawai wadanda basu so ta fadi wannan magana ba amma dole ta fito ta fada dan kada su boye gaskiya.

A'isha Tace duk da cewa gwamnatin Buhari ta samu nasarori da dama amma da ayyukan da zata yi sai sunfi wanda ake gani yanzu in banda wadancan mutanen biyu.

No comments:

Post a Comment