Saturday, 1 December 2018

ALHAMDU LILLAHI AN DAUKI MATAKIN TSARO A SAKKWATO

Bayan Na Yi Rubutun Jan Hankalin Hukumomin Tsaro Da Gwamnantin Tarayya Da Kuma  Ta Jihar Sakkwato, Domin Daukar Mataki Akan Wasu Bakin Haure Dauke Da Manyan Bindigogi Da Aka Ce Sun Bayyana A Jihar Sakkwato. 

Bello Bg Gidanmadi Sokoto Ya Amsa Da Cewa, "Alhamdulillah gaskiya an dauki mataki, domin ni dan Tangaza local govt ne, kuma jiya a gaba na na ga dimbin sojoji dauke da manyan makamai suna wucewa ta garin Gidanmadi zuwa cikin dajin da yan ta'addar suke. 

K'ari ga sojojin da aka tura ranar Talata fatanmu Allah Ya kawo muna karshen su".
Daga Maje El-Hajeej Hotoro.

No comments:

Post a Comment