Sunday, 2 December 2018

Amurka ta yi barazanar kai wa Iran hari

Wakilin Amurka na musamman kan Iran Brian Hook ya bayyana cewa, Idan Iran din ta kuskura ta kai hari kan wani bau mallakar Amurka a yankinta to za su mayar da martani da karfin soji.

A yayin wani taro da aka shirya kan "Taimakon Makamai ga Iran da Habaka Nukiliya" da aka gudanar a birnin Washington ya tabo batun aiyukan da Iran ke aiwatarwa a yankunanta.

Hook ya kuma ce, kungiyoyin da suke yaki a madadin Iran a Yaman, Afganistan, Iraki da Saudiyya na amfani da makan da Iran din ta samar, kuma idan wannan abu da take ya ci gaba, sannan aka ki daukar mataki to hatsarin zai karfafa.

Wakilin na Amurka ya ci gaba da cewa, Iran na ba wa ta'addanci taimako a duniya baki daya. A watannin da suka gabata masu goyon bayan Iran dake dauke da makamai sun kai hari kan ofishin jakdancin Amurka dake Iraki.

Ya ce "Idan Iran ta kuskura ta kai wa wani abu mallakar Amurka hari a yankinta to za ta mayar da martani da karfin soji."

Hook ya kara da cewa, manufar gwamnatin Trump a Gabas ta Tsakiya shi ne dukkan kawayen Amurka sun juyawa Iran baya.

Ya ce, tun shekarar 2007 Iran take ba wa mayakan Taliban taimakon makamai a Afganistan, kuma idan gwamnatin Tehran ta ci gaba da taimaka wa ta'addanci to za su kara kakaba mata takunkunmai masu tsauri.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment