Thursday, 27 December 2018

Amurkawa na tserewa daga manyan biranensu

An bayyana cewar 'yan kasar Amurka na yin hijira daga manyan biranen kasar da sunka hada da Chicago, New York da Los Angeles.


Sabili da hakan wadanan manayan biranen na fuskanatar raguwar al'umma masu dinbin yawa.

Hukumar kidayar jama'a ta kasar Amurka ta fitar da wasu alkaluma dangane da binciken da ta gudanar a shekarar 2017, inda ta bayyana cewar biranen na rasa al'umma ne sabili da hijirar da ake yawan gudanarwa daga biranen.

Alkaluman sun nuna cewa a yayinda a shekarar 2014 mutane dubu 105 da d dari 219 sunka yi hijira daga Chicago a shekarar 2017 yawan wadanda sunka fice daga birnib sun haura zuwa dubu 155 da dari 820.

Ita kuwa birnin New York, a shekarar 2014 ta rana mutane dubu 43 da dari 866, amma a shekarar 2017 yawan wadanda ta rasa zuwa wasu garuruwa sun kai dubu 131 da dari 560.

Birnin Los Angeles kuwa, a shekarar 2014 mutane dubu 12 da dari 392 ne sunka fice daga birnin, a shekarar 2017 kuwa mutanen birnin dubu 127 da dari 630 sunka yiwa birnin kaura.

Mafi yawan wadanda ke ficewa daga biranen mutane ne 'yan tsaka-tsaka wadanda kudin shigarsu a shekara ke tsakanin dala dubu 30 zuwa dubu 60.

Daga cikin manyan dalilan da ke sanya al'umma ficewa daga manyan biranen sun hada da tsadar rayuwa, yawan haraji da kuma karancin karuwar albashi.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment