Wednesday, 26 December 2018

An daurawa 'yan biyun da aka haifa tare mace da namiji aure

Wasu iyaye da suka haifi 'yan biyu mace da namiji a kasar Thailand sun daura musu aure. 'Yan biyun wanda suke da shekaru 6 da haihuwa sun sakawa juna zoben aure yayinda angon ya shiga kofofi shida kamin daga bisani ya ga amaryar tashi ya biya sadaki kuma suka sumbaci juna.


Daily Mail ta ruwaito cewa, mahaifin 'yan biyun, Amornsan Sunthorn Malirat me shekaru 31 ya bayyana cewa wannan al'adace wadda suka gada kaka da kakanni, ana daurawa 'yan biyun daka haifa mace da namiji aurene saboda a addinin Budda sun yi amannar cewa dama tun kamin a haifi irin wadannan 'yan biyun sun kasance masoyan junane sannan kuma idan bayan da aka haifesu ba'a daura musu aure ba to raashin sa'a da ibtila'i kala-kala zai rika fada musu.

Wannan daura aure na al-adane kawai amma zasu iya yin aurensu nan gaba idan suka girma suka hadu da masoya kuma saboda wannan aure da aka daura musu suna yara idan suka girma ba zasu gamu da yawa-yawan rashin lafiya ba kuma zasu yi nasara a rayiwarsu.
No comments:

Post a Comment