Sunday, 16 December 2018

An gano kabarin wani malami na zamanin 'fir'auna'

Masar ta gano hubbaren wani babban jagoran addinin wanda ya kai shekaru kusan dubu hudu da dari biyar da mutuwa.


An dai gano hubbaren ne a daya daga cikin katafaren yankin Saqqara da ake da dalar Masar irin ta zamanin da.

Ma'aikatar adana kayayyakin tarihi ta masar ta ce hubbaren na wani babban malamin addini ne na gidan sarauta da iyalansa a lokacin daula ta biyar ta mulkin fir'aunan.

Bangon hubbaren na dauke da zane mutum-mutumin mutanen gidan da kuma wasu zane-zane na kawa da ke nuna irin wasu ayyukan da sukeyi kamar tuka jirgin ruwa, farautar tsunbtsaye da hadaya.

Sakatare janar na majalisar koli da ke kula da kayyakin tarihi na kasar ta Masar, Dokta Mostafa Al-Waziri, ya ce a hubbaren akwai wasu sako-sako wanda ke nuna cewa akwai alamomin wasu tarin kayayanki tarihi adane acikinsa.

A wannan lahadin dai ake shirin soma aikin tono hubbaren wanda ake saran a sake gano wasu abubuwa tarihi da dama a ciki.No comments:

Post a Comment