Sunday, 2 December 2018

An kama masoyin Tottenham da ya jefi Pierre-Emerick Aubameyang da bawan Ayaba

Bayan da Pierre-Emerick Aubameyang ya ciwa Arsenal kwallo ta farko a wasan da suka buga yau da Tottenham ya kuma je gefen fili yana nuna murnarshi sai aka ga wani bawon ayaba da wani masoyin Tottenham din ya jefo mishi.


Saidai an yi sa'a a yayin da me nuna wariyar launin fatan ke jefo ayabar ashe kyamararnan me ganin kwaf ta daukeshi. Jaridar Mail Online ta tabbatar da cewa an kama mutumin da ma wasu sauran mutane kusan 6 da aka samu da laifin kunna hayaki.

Wasan dai ya kare Arsenal na cin Tottenham 4-2.

Kuma akwai yiyuwar za'a hukunta kungiyar gaba dayanta saboda nuna wariyar launin fatan da wannan masoyin nata yayi.


No comments:

Post a Comment