Monday, 24 December 2018

An kone motocin yakin neman zaben Buhari a kudancin kasarnan

Wasu matasa a jihar Enugu sun kone motocin yakin neman zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari dana mataimakinshi, Farfesa Yemi Osinbajo.


matasan sun kuma kone ofishin yakin neman zaben dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC, Mr. George Tagbo Ogara, lamarin ya farune ranar Asabar din da ta gabata.

Rahoton Premiumtimes yace matasan sun yi amfani da bamabamai wajan yin wannan aika-aika kuma bayan wannan danyen aiki da suka yi sun tsere ba'a kamasu ba.


No comments:

Post a Comment