Monday, 17 December 2018

An saka motar Ronaldo a kasuwa

Motar farko da tauraron dan kwallon kafar kasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya fara saye, kirar Audi S3 a shekarar farko da ya je kungiyar Man United ta shiga kasuwa za'a sayar da ita, saidai abinda yafi daukar hankalin mutane shine zunzurutun kudin da aka tsugawa motar.Ronaldo dai ya sayi motar ta hannu a shekarar 2003 a yayin da yazo kungiyar Man U lokacin yana matashi kuma be damu hawa motoci masu tsada ba.

A yanzu dai an kiyasta cewa motar tana kai Yuro dubu 6 zuwa 10 a kasuwa amma ita wannan ta Ronaldon za'a sayar da ita akan kudi Yuri dubu 20.
AS.

No comments:

Post a Comment