Friday, 7 December 2018

An yi hazon launin shan-shan-bale a Ingila

Wadanda suka yi sammako a safiyar Alhamis a Ingila, sun sha kallo sosai ta yadda rana ta bullo bayan sararin samaniya ya canza zuwa launin shan-shan bale, da ruwan hoda.


Masu hasashen yanayi na BBC suka turo wadannan hotunan daga gabar tekun arewacin Yorkshire har zuwa Dorset inda suke daukar hotunan irin wannan yanayin da ba a saba gani ba.
Mai labarun hasashen yanayi ta BBC watau Sarah Keith-Lucas ta bayyana cewa daya daga cikin abinda yasa aka samu haka shi ne sauyin yanayin da aka samu ne daga bangaren tekun Atlantika.
Ya kuma bayyana cewa "Karin iskar da ke tashi zuwa teku, zai iya ja a samu kwayoyin gishiri zuwa sararrin samaniya," hakan yake ja haske yana kara watsuwa sosai, sai ya sa a samu tsayayyun launi irin ruwan hoda da shan-shan bale a lokacin fitowar rana da faduwarta.
Dalilin da yasa launin sama yake canzawa- inji Sarah Keith-Lucas, ma'aikaciyar BBC a bangaren hasashen yanayi.

Gajeren ratsin shudi da kuma launin shan-shan bale yana saurin watsuwa, amma dogon ratsin ruwan lemo da kuma ja basu sauran watsuwa, saboda haka suke ratsa idanuwanmu.
Wannan yana nufin sararin samaniya kan koma launi ja, ruwan hoda ko kuma ruwan lemu a lokacin fitowa da faduwar rana.

Ana samun takamaiman laununkan da ake samu ne a lokacin fitowar rana a bisa dalilan kura, gurbacewar muhalli, yayyafi da kuma haduwar giza-gizai, a wani lokacin za su iya zama ruwan shan-shan bale da ruwan hoda ba wai lallai sai ruwan lemu ko ja kamar yadda aka fi sani ba.

Wannan zai iya zama daya daga cikin abinda idonmu yake nuna mana, na ratsin ruwan hoda da ke haskaka sararin samaniya, haka kuma wadannan giza-gizan masu ruwan hoda suna ratsa giza-gizai masu launin shudi.

Haduwar ruwan hoda da na shudi kan saka sararin samaniya ya zama ruwan shan-shan bale.BBChausa.

No comments:

Post a Comment