Monday, 24 December 2018

Ana zanga-zangar nuna damuwa da yawaitar kashe-kashe a Zamfara

Al'ummar jihar Zamfara a arewacin Najeriya na gudanar da zanga-zanga domin nuna damuwa da yawaitar kisan rayuka da ake yi a sassan jihar.


Ana gudanar da zanga-zangar ne a karamar hukumar mulki ta Tsafe, da ke nisan kusan kilomita 50 da Gusau babban birnin jihar.
Rahotanni sun ce matasa da 'yan gudun hijira da suka kunshi mata da yara kanana sun toshe babbar hanyar da ke zuwa Gusau, tare da kone wasu gine-ginen gwamnati.
Rundunar 'yan sandan jihar da ta tabbatar da faruwar al'amarin ta ce ta kama wasu daga cikin masu zanga-zangar kamar yadda kakakin 'yan sandan DSP Muhammad Shehu ya shaida wa BBC.
Mazauna garin na tsafe na bayyana damuwa ne kan yadda masu gudun hijira ke ci gaba da tururuwa a yankin, suna guduwa sakamakon hare-haren da ake zargi yan bindiga da barayin shanu ke kai wa.
Masu zanga-zangar sun bayyana cewa, sun gaji da halin ko-in-kula da hukumomi suke nunawa a kan rashin tsaro a jihar.
Shugaban karamar hukumar Tsafe Alhaji Abubakar Aliyu ya shaida wa BBC cewa, sama da mutum 40 ne suka rasa rayukansu a kauyuka daban-daban cikin mako biyu.
A makon da ya gabata ne, aka kashe mutane da dama a wani hari da aka kai a kauyen Birnin Magaji, inda nan ne kauyen da minstan tsaro a Najeriya ya fito.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment