Saturday, 8 December 2018

Arsenal na bincike kan faifan bidiyon da 'yan wasansa ke shaye-shaye


Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta ce ta na gudanar da bincike kan yadda aka nuna wani faifan bidiyo da ke nuno 'yan wasanta na shakar wani sinadari mai hayaki, duk da ya ke baya cikin sinadarin da aka haramtawa 'yan wasa amfani da shi.


Faifain ya nuna yan wasa 4 da suka hadar da Alexander Lazcazette da Matteo Guendouzi da Mesut Ozil da kuma Pierre Emerick Aubameyang, na shakar sinadarin lokacin da suka ziyarci wani gidan rawa a birnin London.

Masana sun ce shakar irin wannan hayaki da yawa na iya hana kai iskar numfashin da ake shaka zuwa kwakwalwa.

A cewar Club din yanzu haka yana ci gaba da bincike kan faifan bidiyon don daukar matakan da suka dace.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment