Saturday, 1 December 2018

Atiku ya samu takardar izinin shiga kasar Amurka

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya samu takardar izinin shiga kasar Amurka da aka dade ana ta cece-kuce kai.


Jaridar The Cable tace ta samu wani na kusa da iyalin Atikun ya tabbatar mata da wannan labari.

Haka kuma ta kara da cewa, ta samu tabbacin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjone ya shigewa Atikun gaba wajan samun takarar izinin shiga kasar ta Amurka.

Atiku dai ya jima, kusan shekaru 13 kenan be shiga kasar Amurka ba, abinda aka rika alakantashi da cewa yana gujewa kamun da jami'an kasar ke shirin mishine akan zargin cin hanci.

No comments:

Post a Comment