Monday, 24 December 2018

Atiku ya taimakawa wata yarinya da bata da lafiya a garin Daura

Sanannen me rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta dan kare muradun gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ake kira sa Datti Asalafi a wannan karin ya yabi dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar saboda taimakon wata yarinya da yayi da bata da lafiya da ta fito daga garin Daura.


Datti yayi rubutu kamar haka:
ALHERIN ALLAH YA KAI GA DATTIJO MAI TAUSAYIN TALAKAWA ALHAJI ATIKU ABUBAKAR

Daga Datti Asslafiy

Jama'a idan za ku tuna kwanaki uku da suka gabata mun fitar da sanarwa na wata yarinyar marainiya 'yar shekara 13 da haihuwa, sunanta Aisha Haruna da take tare da mahaifiyarta a unguwar Rahamawa dake garin Daura jihar Katsina wacce ta hadu da tsautsayi na kunar wuta wanda ya mata illa sosai, mukace aje a bincika a tabbatar don a tallafa mata.

AlhamdulilLah bayan Baba Atiku Abubakar yaga sanarwan ya tura wakilcin kungiyarshi na "Atiku Care Health Foundation" sun dauki nauyin jinyar yarinyar, daga karshe sun dauke ta daga garin Daura suka kaita asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano  (Aminu Kano Teaching Hospital).

A halin yanzu har an mata aiki kuma tana  samun lafiya sosai.

Mutanen mu da muke tsammani za su taimaka wa rayuwar yarinya sun kasa yin komai kansu kawai suka sani, sai 'yan adawarmu a siyasa ne sukayi

Baba Atiku mungode kwarai dagaske bisa ceto rayuwar marainiyar Allah da ka yi. Kai ma muna maka fatan Allah Ya cece ka ranar hisabi, Allah Ya biya maka dukkan bukatunka na alheri.

No comments:

Post a Comment