Wednesday, 26 December 2018

Atiku Ya Tallafawa 'Yan Gudun Hijirar Jihar Zamfara Da Kayan Masarufi

Gidauniyar tallafawa marasa galihu ta 'Atiku Care Foundation' ta tallafawa daruruwan 'yan gudun hijira a jahar Zamfara.Gidauniyar tana gudanar da aikin ta tsawon lokaci wajen bada tallafin kayan abinci ga masu bukata musanman marayu masu rangwamen gata da ‘yan gudun hijira wadanda ‘yan ta’addan Boko-Haram suka raba su da gidajen su a jihohin Borno, Adamawa da Yobe. 

Al’ummar jihar Zamfara ma da iftila’in ‘yan ta’adda ya fada masu su ma sun rabauta da irin wannan tallafin kayan masarufi da suka hada da shinkafa, taliya da man gyada daga gidauniyar ta 'Atiku Care Foundation'.

No comments:

Post a Comment