Sunday, 2 December 2018

Atiku yaje shiga kasar Amurka amma ya fasa ya dawo gida saboda tsoron kamu

A jiyane muka ji cewa, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya samu takardar izinin shiga kasar Amurka bayan shafe shekaru 13 be shiga kasar ba bisa zargin kamu akan wasu badakalar kudi, kamar yanda The Cable ta ruwaito.


Haka kuma anji cewa Atikun yaje kasar Ingila inda daga canne ake tsammanin zai shiga kasar ta Amurka.

Saidai labarin dake fitowa daga kafar PM News na cewa Atikun yaje kasar Ingilane dan a tabbatar mai cewa idan ya shiga kasar Amurka ba za'a kamashi ba amma binciken da aka mai be bashi wannan tabbaci ba shiyasa ya dawo gida Najeriya abinshi.

No comments:

Post a Comment