Tuesday, 4 December 2018

Atiku yayi magana akan maganar cewa wai an canja Buhari

Dan takarar shugaban kasa, Karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya mayar da martani akan rade-radin dake yawo tsakanin wasu 'yan Najeriya na cewa, wai an canja shugaba Buhari ba wanda aka sani bane.


Me magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Atikun, Osita Chidoka ne ya bayyana haka a wata hira da yayi a gidan talabijin din AIT a wani shiri me suna Kakaaki.

Yace matsalar da aka samu itace, fadar shugaban kasa ta yi gum akan rashin lafiyar shugaban kasar, mutane basu san ainihin ciwon dake damun shugaban ba, a wane asibiti aka dubashi, wane likitane ya dubashi dadai sauransu

Ya kara da cewa ya kamata majalisa ta fito da wata doka akan irin wannan yanayi tunda fadar shugaban kasa ta gaza.

No comments:

Post a Comment