Saturday, 1 December 2018

Auren gama-gari a Zirrin Gaza mai ƙayatarwa

A garin Ramallah an gudanar da gagarumin bukin auren gama-gari mai ƙayatarwa har na angwaye da amare 117 a Zirrin Gaza. 


Bukin ya samu halartar shugaban kasar Falasɗinu Mahmud Abbas da kuma shugabanin kungiyar kare hakkin Falasɗinawa da manyan jami'an gwamnati.

Shugaba Abbas ya yiwa ma'auratan kyauta da ya ƙunshi harda na kuɗaɗe.

Shugaba hurɗar jama'a a fadar gwamnati Falasɗinu Gassan Nimr ya bayyana cewar an zabi ma'auratan ne bisa wasu ƙaidoji da suka haɗa da mallakar kudi da kuma wasu lamurkan yankin.

Nimr ya bayyana cewar za'a dinga gudanar da wannan auren gama-garin a ko wacce shekara a ƙasar. Ana shirin mayar da wannan muhimmin auren mai ban sha'awa al'adan kasar.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment