Sunday, 2 December 2018

'Ba da zuciya daya gwamnati ke raba kudin tallafi ba'

Shugaban majalisar dattijan Najeriya Sanata Bukola Saraki ya soki matakin gwamnatin tarayyar kasar na raba kudi ga kananan 'yan kasuwa da sunan tallafi.


A cewar Saraki, wanda tsohon dan jam'iyyar APC mai mulki ne, da alamun cewa gwamnatin tana da wata manufa ta daban, baya ga abinda ta ce tana yi da kudin.

Ya ce "Wannan shiri (Trader Moni) ya dade da aka tsara shi, shekaru biyu da suka gabata. A shekarar 2015 ban ga mataimakin shugaban kasa na zuwa ya na bai wa 'yan kasuwa kudi ba, haka kuma bai yi a 2016, da 2017 ba, sai a 2018".

Ya kara da cewa "Abu mafi muni shi ne (Mataimakin shugaban kasa) na tafiya ne da shugabar mata ta jam'iyyarsa(APC), da gwamnoni na jam'iyyarsa. Kamata ya yi ya tafi da shugabannin mata na dukkan jam'iyyun Najeriya, saboda kudi ne na 'yan kasa. Wannan kuskure ne. Wannan wata dubara ce. Idan ba wata manufa ai da sun yi haka tuntuni, amma ba su yi ba sai yanzu a shekara ta 2018".

Sanata Bukola Saraki dai ya yi wannan zargin ne a wani taro na manema labaru.

Sanatan kuma shi ne wanda babbar jam'iyyar adawa a kasar (PDP) ta nada a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugabancin kasar a karkashin ta, wato Atiku Abubakar.

To sai dai gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan wannan zargi.

A cewar Dakta Bilisu Sa'idu mai taimaka wa mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo kan harkar shari'a, tallafin 'Trader Moni' wani shiri ne da gwamnati ta bullo da shi domin cika alkawarin da ta yi wa al'ummar kasar a lokacin yakin neman zabe.

Ta ce 'Daya daga cikin alkawurran da aka yi wa al'umma shi ne gwamnati za ta fito da wani tsari, wanda zai taimaka wa 'yan kasa wadanda ke da karamin karfi domin su samu dogaro da kansu".

Ta kuma ce abin mamaki ne yadda wasu ke sukar gwamnati saboda tana kokarin cika alkawarin da ta yi wa al'umma kafin zabe.

Ta kara da cewa gwamnatin tana bayar da kudin ne a matsayin bashi ga al'umma, ba kyauta ba.

A game da zancen ko ana bayar da kudin ga magoya bayan jam'iyyar APC ne, Dakta Bilkisu ta ce "Ba a tambayar mutum ko yana da katin zabe, maganar ba ta da tushe balle makama".

Sannan kuma a cewar ta majalisar dokokin kasar ce ta amince a fitar da kudin domin aiwatar da shirin.

Gwamnatin Najeriya ce ta ce za ta yi amfani da shirin na 'Trader Moni' wurin tallafa wa mutane miliyan biyu, masu karamin karfi a kasar.

A karkashin shirin gwamnati takan bayar da bashin Naira dubu goma (Kimanin dala 28) ga kananan 'yan kasuwa a matsayin bashi.

An sha ganin mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo yana zuwa kasuwanni a jihohi daban-daban na kasar domin kaddamar da raba irin wadannan kudade ga kananan 'yan kasuwa.

Sai dai tun bayan fara shirin, wasu mutane, musamman daga bangaren jam'iyyun adawa na kasar ke nuna damuwa kan yadda ake gudanar da shi, inda suke zargin ana sanya siyasa, abinda gwamnatin kasar ta sha musawa.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment