Tuesday, 4 December 2018

Ba Zan Kuma Korafi A Kan Matsalar Nijeriya Ba>>Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa ba zai kara korafi ba a kan matsalolin da gwamnatinsa ta tarar a kasar nan a lokacin da ta dare karagar mulki. 


Shugaban kasar ya ce koken da suka yi ta yi a baya kan cin hanci da rashawa da kuma wadaka da dukiyar al'ummar da gwamnatocin baya suka yi bai wani taimaka wa gwamnatinsa ba, don haka yanzu kawai zai fuskanci matsalolin kai tsaye ba tare da wani karin gunaguni ba. 

Ya bayyana haka yayin da yake tattaunawa da 'yan Nijeriya mazauna kasar Poland, yayin da ya je kasar domin halartar babban taro a kan canjin yanayi.

Shugaba Buharin yake cewa, "Mun gaji da matsaloli masu tarin yawa, amma a zahiri na ce ba zan yi korafi a kai ba saboda ni na nema. Na yi kokarin zamowa shugaban kasa sau uku amma ban samu nasara ba. Sai a karo na hudu na samu nasara, na zamo shugaban kasa, saboda haka ba zan iya korafi ba. 

"Wane ne ya ce min in kuma yi? Sau uku ina karewa a kotun koli. A karo na uku na ce Allah yana nan, sannan a karo na hudu da taimakon Allah da kuma fasahar zamani, ta hanyar amfani da katin zabe na dindindin da na'urar 'Card Reader', ba su iya murde zaben ba, saboda haka na samu nasara."
Sarauniya.

No comments:

Post a Comment