Saturday, 22 December 2018

Badeh Ya Hadu Da Aisha Buhari Da Kyari Kafin A Kashe Shi

Jaridar Punch ta yi rahoton cewa tsohon babban hafsan tsaron Nijeriya, Air Chief Marshal Alex Badeh ya gana da Aisha, uwar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, da kuma shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, game da shari'ar da ake da shi kan laifin cin hanci da rashawa, sati uku kafin wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ba su harbe shi har lahira a kan hanyar Abuja zuwa Keffi, ranar Talata. 


Jaridar ta yi rahoton cewa ta gano cewar wai Badeh, wanda ke fuskantar tuhuma kan handame wasu makudan kudade mallakin rundunar sojin saman Nijeriya, ya hadu da Aisha Buhari domin ya roke ta kan ta sanya baki a cikin tuhumar da kotu take masa ta handame wadannan makudan kudaden.

Wani makusancin mamacin ya yi ikirarin cewa ya rada masa cewar Aisha Buharin ta gaya masa cewar Kyari ne kawai zai iya taimaka masa.

"Badeh ya fadi cewar daga nan Aisha Buhari ta dauke shi zuwa gurin Kyari, amma shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar bai nuna alamar gamsuwa ko rashin ta ba. Ya ce da tsohon hafsan tsaron da ya kira shi a waya, amma sam ya gaza samun Kyarin a waya tun da suka yi mitin din a sati uku da suka wuce," majiyar, wanda tsohon jami'in aikin damara ne ya fada. 

Sai dai kuma akwai wasu alamomi masu karfi da ke nuna yuwawar hukumar EFCC ba za ta daga wa kadarorin Badeh kafa ba duk da cewar ya riga mu gidan gaskiya. 

Wani jami'in hukumar ta EFCC wanda bai bari a ambaci sunanshi ba ya ce hukumar ta yi niyyar ci gaba da shari'ar da ake da mamacin har zuwa karshe domin ta karbo dukkan kadarorin da ya tara ba bisa doka ba.

No comments:

Post a Comment