Sunday, 23 December 2018

Balarabe Nass da 'yan Najeriya ke kuskurewa a matsayin majalisar tarayya yayi rubutu da Hausa

An tashi da mamaki a dandalin Twitter bayan da shahararren balarabennan me amfani da Nass da 'yan Najeriya ke kuskurewa a matsayin majalisar tarayya yayi rubutu da Hausa.


A baya dai dama Nass yayi rubutu da Pidgin inda har wasu suka fara shakkun cewa kodai wani dan Najeriyar ne ke amfani da shafin na Nass a matsayin balarabe?

Kwatsam kuma sai gashi yayi runutu da Hausa inda ya rubuta, An tashi lafiya?

Wannan lamari ya dauki hankula.

No comments:

Post a Comment