Monday, 24 December 2018

Ban kira matar Sakaba ba, kuskure aka samu>>Atiku

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2019,Atiku Abubakar ya fito ya amsa cewa bai kira matar marigayi Lt. Col. Sakaba ba da ya rasa ranshi a harin Metele da Boko Haram suka kai.


Bayan da Atiku ya bayyana ta shafinshi na dandalin sada zumunta cewa ya kira matar Sakaba, Punch ta ruwaito cewa matar, me sun Seun ta ce ita Atiku be kirata ba kuma ta yi mamakin yanda dan siyasa me shekaru 72 zai yi karya irin wannan.

Vanguard ta ruwaito cewa, Atiku ya fitar da sanarwa inda ya amsa cewa kuskure aka samu a sakon da ya fitar.

Yace, bayan harin Metele, ya bukaci ma'aikatanshi da su nemo mai lambar matar Sakaba dan ya mata ta'aziyya.

An samo lambar tata da ta kanwar Sakaba din me suna Maryam.

Atiku yayi kokarin kiran matar sakaba amma bai samu ba shine sai ya kira kanwarshi Maryam ya mata ta'aziyya.

Atiku yace kuskure aka samu kuma yana kara mika ta'aziyyarshi ga iyalan na Sakaba.

No comments:

Post a Comment