Saturday, 15 December 2018

Barcelona ta hana Dembele kashe wayarshi ko kuma cire karanta

Kungiyar Barcelona ta sakawa matashin dan wasanta, Ousmane Dembele wata doka da ta dauki hankulan mutane inda wasu ke cewa ta yi tsauri da yawa.


Dokar dai itace kungiyar tace bata yadda Ousmane Dembele ya kashe wayarshi ba ko kuma ya cire karan ta ba da dare.

Wannan na zuwane a matsayin horo bayan da aka cajeshi Faan dubu 90 dalilin zuwa a makare gurin atisaye da kuma gurin buga wasa da kin halartar taron musamman na kungiyar da kuma kin zuwa motsa jiki.

Marca ta ruwaito cewa, Barcelona na kokarin ganin ta kawar da dabi'ar yawan son buga wasan Game da kuma kallon fina-finai da dan wasan ke yi da dare dan haka ta hanashi kashe wayarshi dan ya rika jin karaurawar tada shi daga bacci.

Barca dai tana son yi da Dembele saboda kokarinshi wajan cin kwallaye, haka kuma sauran abokan wasanshi sun bayyana cewa suna bukatarshi kuma zasu taimakamai ya dawo daidai saboda kuruciyace ke damunshi.


No comments:

Post a Comment