Wednesday, 26 December 2018

Bikin Kirsimeti: Buratai ya zubawa sojoji abinci

Shugaban sojin kasa na Najeriya, Tukur Yusuf Buratai kenan a wadannan hotunan tare da manyan sojoji suje rabawa sojan dake rundunar Operation Lafiya Dole dake yaki da Boko Haram a Arewa maso gabas Abinci a bikin Kirsimeti da ake ci gaba da yi a yau, Laraba.A jawabinshi a gurin cin abincin Kirsimetin, Buratai ya yiwa sojojin da suka rasa rayukansu addu'a sanna kuma ya yabawa wanda sukenan bisa juriya da nuna kwazo.

Ya tabbatar musu da cewa mutanen Najeriya suna yabawa da aikin da suke yi kuma shugaban kasa yayi alkawarin ci gaba da basu goyon bayan da duk ya kamata, ya kuma ce tabbas sun ci karfin Boko Haram sannan kada su yadda da labaran karya da farfagandar da Boko Haram din ke yadawa da niyyar kashe musu karfin gwiwa.

Yace sun yi nasara sosai a yaki da ta'addanci a kasarnan abinda ya rage kawai shine kakkabe sauran birbishin Boko Haram da ya rage ta amfani da dabarun yaki.

No comments:

Post a Comment