Saturday, 15 December 2018

Buhari abin koyi ne ga matasa>>IBB

Tsohon shugaban kasar mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya taya shugaban kasa, Muhammadu Buhari murnar cika shekaru 76 a Duniya.


A cikin sakon taya murnar da jaridar The Sun ta samu, IBB ya bayyana shugaba Buhari a matsayin shugaba wanda ya zama abin koyi ga matasa musamman 'yan siyasa masu son rike ragamar kasarnan.

Ya kuma yabi gwamnatin Buharin akan ayyukan da take yi na Yaki da cin hanci da Rashawa da kuma maganar kawo tsaro da kuma fitar da Najeriya daga kangin matsalar tattalin arziki, ya bayyana shugaba Buhari a matsayin dan kishin kasa kuma me gaskiya.

A karshe ya taya Buharin murnar cika shekaru 76 inda ya kuma yabawa A'isha Buhari bisa kula da gida

No comments:

Post a Comment