Monday, 24 December 2018

Buhari na maimaita irin kuskuren da Jonathan yayi

Malamin jami'a, Dr. Aminu Gamawa yace, lokacin mulkin Jonathan mun sokeshi da PDP da ci gaba da yakin neman zabe a yayin da ake ganiyar kashe mutane.


Yace, gashi a yau, Buhari da APC na maimaita irin wancan kuskure, ya kara da cewa, wasu masu makauniyar soyayya ba sa ma so a rika maganar kashe-kashen da ake yi a Zamfara da sauran gurare. 

Dole gwamnatin tarayya ta kawo karshen wannan kashe-kashe.

No comments:

Post a Comment