Sunday, 2 December 2018

Buhari ya karyata rade-radin cewa an canjashi a ganawar da yayi da 'yan Najeriya mazauna Poland

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari kenan a wadannan hotunan yayin da yake ganawa da 'yan Najeriya mazauna kasar Poland, shugaban dai ya je kasar ta Poland ne dan halartar taron canjin yanayi.


A ganawar shugaba Buhari ya karyata rade-radin dake yawo cewa wai an canjashi bashi bane na ainihi, yace, wasu da dama sun yi fatan cewa na mutu a lokacin da na yi rashin lafiya nine da kaina kuma kwananan zan yi bikin cikata shekara 76 da karfina.


No comments:

Post a Comment