Monday, 3 December 2018

Da Yardar Allah Sai PDP Ta Kwace Mulki Daga Hannun APC>>Buba Galadima

PDP wadda ita ce babbar jam'iyya mai hamayya da jam'iyyar APC mai mulkin kasar ta kaddamar da babban kwamitin yakin meman zabe na dan takarar shugabancin kasa Atiku Abubakar.


Sai dai baya ga jiga-jigan jam'iyyar ta PDP, kwamitin ya kunshi kusoshin wasu jam'iyyun hamayya, irin su Injiniya Buba Galadima wanda ke ikirarin shi ne shugaban gangariyar jam'iyyar APC, wato rAPC.

Ita dai rAPC wadda Buba Galadima ke wa jagoranci ta balle ne daga jam'iyyar APC mai mulkin kasar, sa'ilin da aka samu sababin ra'ayi tsakanin 'ya'yanta.

Buba Galadima ya yi wa BBC karin bayani game da dalilin da ya sa yake cikin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, wanda shi ne ake ganin fafatawa za ta fi zafi tsakanin sa da shugaban Nijeriya mai ci Muhammadu Buhari.

Ya ce za su yi aiki tukuru wajen tabbatar da cewa an dawo da Najeriya bisa tafarkin da ya dace kamar yadda suka yi aiki tukuru wajen ganin APC ta kafa gwamnati a zaben da ya gabata.

Sai dai ya tabbatar da cewa rAPC din har yanzu tana nan a matsayin jam'iyya mai zaman kanta.

Galadima ya yi ikirarin cewa a halin yanzu Nijeriya ba ta tafiya bisa tafarkin da ya dace.

Ya ce "Nijeriya ba ta tafiya daidai, tana tafiya a karkace, saboda haka dole mu gyara ta".

Ya kuma ce babu tantama Insha Allahu PDP za ta kwace mulki daga hannun jam'iyyar APC.
Rariya.

No comments:

Post a Comment