Thursday, 27 December 2018

Dalibar jami'ar ABU, A'isha ta kashe kanta saboda tsangwamar mahaifiyarta

Wannan wata baiwar Allah ce me suna A'isha Omolola dalibar jami'ar Ahmadu Bello, ABU dake Zaria, rahotanni sunce ta sha guba ta kashe kanta saboda takaicin kiyayyar da mahaifiyarta ke nuna mata.


Shafin Instablog ya wallafa labarin A'isha da sakon takardar data bari inda ta rubuta yanda mahaifiyarta take kiranta da mayya kuma duk kokarinta na farantawa mahaifiyaratata ya tashi a banza bata gani.

A'isha ta kara da cewa tana da dan uwa amma shima be damu da ita ba.

Allah shi kyauta.

No comments:

Post a Comment