Sunday, 16 December 2018

Dalilai 12 da zasu sa a sake zaben Buhari>>Daga Garba Shehu

A wata sanarwa da ya fitar, Me magana da yawun shugaban kasa, malam Garba Shehu ya bayyana dalilai da zasu sa a sake zaben shugaban a zaben 2019.


Ya fara da cewa ba'a taba samun shugaba na gari irin shugaba Buhari ba a kasarnan sannan kuma shugaban yana da kyakkyawar dabi'a.

A Duniya gaba daya an tabbatar da cewa, shi shugabane me gaskiya wanda kuma yake aiki tuku dan ganin ya warkar da kasarnan daga ciwon da shuwagabannin baya suka mata.

Yana da nutsuwa da yadda dakai wajan gudanar da ayyukanshi.

A duk lokacin da aka sokeshi a kan gwamnatinshi baya kidimewa ya rasa nutsuwar da yake da ita.

Yakan yi amfani da barkwanci wajan mayar da martani ga sukar da ake mai.

Da dama sun kirashi da me tafiyar hawainiya a rashin fahimtar cewa yana gudanar da ayyukanshine bisa tsanaki da sanin ya kamata.

Dalili na gaba da zai sa a zabi Buhari shine yaki da cin hanci da yake yi wanda shuwagabannin baya suke baiwa CBN umarnin kwaso kudi a raba a tebur.

Yanzu an kwato dajin Sambisa daga hannun Boko Haram kuma kanfanonin sufurin jiragen sama sun koma aiki a Maiduguri.

Kungiyar kiristocin Najeriya, CAN ta tabbatar da cewa kirsimetin 2017 itace suka yi cikin mafi kwanciyar hankali.

Da dama daga wanda Boko Haram suka sace yanzu an dawo dasu gida da suka hada da 'yan matan Dapchi, dana Chibok da malam jami'a dadai sauransu.

Fannin wutar lantarki an samu ci gaban me ban mamaki.

Shugaba Buhari yana da karfin fada aji a Duniya lura da yanda ya jawo hankulan kasashen Duniya dake fitar da mai suka daidaita farashin danyen mai a Duniya.

Shugaba Buhari ne ke jagorantar yaki da cin hanci a nahiyar Africa.

Wadannan dalilai dama wasu da dama sun isa su sa a sake zabar Buhari shugaban kasa,inji Garba Shehu kamar yanda Vanguard ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment