Thursday, 27 December 2018

Dole Buhari ya rika kirana da ranka shi dade har in mutu: Kuma da ban goyi bayanshi a 2015 ba da baici zabeba>>Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa da fa be goyi bayan shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2015 ba da be ci zabe ba.


Ya bayyana hakane a gurin wani taro a Jihar Ogun, ya kara da cewa dole ya yiwa Buhari gyara a al'amuran mulkinshi saboda ya kai matsayin da zai mai gyaran tunda ya taba mai kuma ya bayar da jininshi dan Najeriya.

Ya ce har ya mutu dole Buhari ya ci gaba da kiranshi da ranka shi dade, yace, Abubuwa basa tafiya yanda ya kamata a kasarnan kuma dole yayi magana dan yasan Allah ya albarci Najeriya da duk abinda take bukata.

No comments:

Post a Comment