Saturday, 22 December 2018

Eedris Abdulkareem zai yi wakar Jagajaga ta biyu

Tauraron mawakinnan, Eedris Abdulkareem ya bayyana cewa nan bada dadewa ba zai saki wakar Jagajaga ta biyu.


Kusan shekaru 15 kenan da yin wakar ta farko, mawakin ya bayyana cewa amma kusan matsalolin da ake da su basu canja ba sai ma karuwa da suka yi.

Ya saka dandanon sabuwar wakar a dandalinshi na sada zumunta inda yace nan gaba kadan zai saki ainahin wakar.

No comments:

Post a Comment