Sunday, 2 December 2018

Fadakarwa akan neman mace dan Allah

Wallahi duk Wanda ya yaudari kanshi yana neman macce dan kyawonta, ko yana neman macce saboda 'yar su wane ne, ko yana neman macce saboda kaza dinta........ 
Wallahi ba shakka kana 6ata ma kanka lokaci ne, ka nemi ma'aurata su gayamaka Wanda ya auri macce dan kyawonta ya gayamaka harajin nawa yake biya dan wannan kyaun nata...... 

Haka kuma Wanda ya auri macce dan 'yar wane ne, ko 'yar uwar su wane ne kaje ya gayamaka bala'in dayake gamuwa dashi da wulakanci da cutuwa a wajenta saboda ba dan Allah ya aureta ba........

Ma'aiki (SAW) yace Ana auren macce dan Addininta, dan Nasabarta, dan dukiyarta, dan kyawonta....

Amma Mafi alkhairi Wanda ya auri macce dan Addininta.... 
Allah yasa mudace.
Daga A'isha Umar.

No comments:

Post a Comment