Saturday, 8 December 2018

Fadakarwa da karfafa gwiwa akan halartar sallar Asuba a wannan yanayi

Tauraron me fadakarwannan a shafin Twitter, Mustafa wanda aka fi sani da Angry Ustaz ya tunatar da mutane akan muhimmancin sallar Asubahi. Ya fara da cewa, akwai sanyi me tsanani kuma sahabbai na makyarkyata/karkarwa amma a haka suka tsayu dan biyayya ga Allah a yakin khandaq.


Ya kara da cewa, abin da suke buri shine yardar Allah dan su samu shiga Aljanna.

Amma a yau muna rasa sallar Asuba saboda sanyi kuma irin Aljannar da suke nema muma muke nema.
Mustafa ya kuma karfafa gwiwa akan halartar sallar Subahi cikin jam'i inda yace, babu dadi mutum ya tashi da sassafe a cikin wannan sanyin, ya bar dumin iyalinshi ko bargo(ga gwauraye) ya tafi masallaci halartar sallar Asuba.

Ya kara da cewa, Wallahi ba dadi amma idan ka tuna da ladar da zaka samu(Aljannah) inda zamu ji dadi da hutu na har abada sai kaji abin ya zo da sauki.

No comments:

Post a Comment