Thursday, 27 December 2018

Fadar shugaban kasa ta bayyana mutanen dake juya Buhari

Fadar shugaban kasa ta hannun me magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu ta mayar da martani akan zargin da ake yi na cewa akwai wasu masu juya shugaban kasar yadda suke so, bashine ke tafiyar da mulkin kasarnan ba.


Garba yayi magana da manema labaraine a fadar shugaban kasa jiya, Laraba kamar yanda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Yace, ba kamar yanda aka saba samun masu juya shugaba a gwamnatocin baya ba,  mutanen Najeriya miliyan 200 sune ke juya shugaba Buhari, duk wata magana da shawara da zai yanke yana yintane da la'akari da mutanen Najeriya a ciki.

Ya kara da cewa, jam'iyyar adawa ta PDP ta guji saka sunan uwargidan shugaban kasa a sukar da take mai, idan kuma suna so ne a rika sako maganar iyalin mutum a yakin neman zabe to APC a shirye take ayi hakan.

Yace PDP bata da wani abu da zata nunawa 'yan Najeriya a shekaru 16 da ta yi tana mulkin kama karya, babu ayyukan raya kasa, babu tsaro, sun samu kudi wajan sayar da danyen mai amma basu yi komai dasu ba, sun fitar da kudi dan a gyara wutar lantarki amma ba'a samu wutar ba.

Yace PDP ta kaddamar da yakin neman zabenta amma be dauki hankulan mutane ba, suna ta taro amma 'yan tsirarun mutanene ke fitowa, yace wai jam'iyyar da take ikirarin cewa itace mafi girma a nahiyar Africa ce take bi tana rokon kananan jam'iyyu dan su goya mata baya, yace PDP bata da abinda zata nuna ta ci galaba a kan Buhari a aikace.

No comments:

Post a Comment