Thursday, 6 December 2018

Ghali Na Abba ya fice daga APC yace basu san inda suka dosa ba

Tsohon kakakin majalisar wakilai, Ghali Umar Na Abba ya bayyana ficewarshi daga jam'iyya me mulki ta APC bisa dalilan rashin Alkibla da jam'iyyar keda shi.


Na Abba a cikin wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa, duk me ido zai iya ganin cewa APC na kokarin kai Najeriya ga hanyar ni 'yasu ne da kuma rashin tabbas.

Yace akwai girman kai da rashin sanin inda aka dosa da kuma rashin iya aiki dake damun wannan gwamnatin, ya kara da cewa matsalar dake APC dinne yasa ta rasa jigoginta irin su shugabannin majalisun tarayyya.

Ya zuwa yanzu dai be bayyana jam'iyyar da ya koma ba

No comments:

Post a Comment